Jama'a da dama na tunanin cewa yin anfani da shafin nan na sada zumunta da aka fi sani da twitter an kirkiro shi ne saboda matasa kawai ko kuma tamkar bata lokaci ne a wurin wasu, wasu ma sun dauke ta a matsayin wata sabuwar hanyar yada jita jita ko gulmace gulmace kawai.
Amma bincike ya nuna cewar wannan kafar sadarwa ta wuce yadda mutane suke tunani domin kuwa, ainihin manufar ta ita ce kafar sadarwar da ke son cimma burin wanda ya aika da sakon ba tare da bata lokaci ba.
Hanyar da zata sada mai anfani da ita da duniya cikin 'yan dan kankanen lokaci ce, kuma zata baka masaniya akan duk abubuwan da ke faruwa a fadin duniya ba tare da mutum ya je wani wiri ba.
Sama da mutane miliyan 316 ke anfani da Shafin sadarwar Twitter a kowane wata daga dukkan kusurwoyin duniya.
Idan baka anfani da wannan shafin zumunta, za ka yi mamakin dalilan da yasa wannan shafin yake da tasiri a kamar sauran shafukan yada zumunta.
Shafin Twitter zai ba mai anfani da shi damar sanin abubuwan da ke wakana a fadin duniya nan take a lokacin da abin ke faruwa. Idan wani abu na faruwa a Najeriya nan take wanda ya ke Landan ko Amurka da sauran fadin duniya za su sami labari.