A Nigeria Senata Aisha Jummai Alhassan ita kam ta shiga tarihi a zaman macen farko da aka zaba gwamna bisa tafarkin mulki democradiya, bayan da wata kotun daukaka kara a Abuja baban birnin taraiyar Nigeria ta ayyana ta a matsayin gwamnar jihar Taraba.
Senata Aisha Jummai Alhassan ta godewa Allah da dukkan magoya bayanta da suka taimaka da adu'a da wasu abubuwa a hira da wakiliyar sashen Hausa Medina Dauda ta yi da ita
Your browser doesn’t support HTML5
Senata Aisha Jummai Alhassan akan nasarar data samu 1.59
Haka suma shugabanin kungiyoyin mata da suka halara a gidan Senata Aisha bayan da kotun daukaka kara ta yanke hukunci, suna taya ta murna, sun baiyana jin dadin su kamar haka
Your browser doesn’t support HTML5
Ra'ayin wasu mata akan nasarar da Senata Jummai Alhassan ta samu 2.41