Sabuwar Dokar Hana Talla A Legas

Wata sabuwar doka da gwamnatin jahar Lagos ta kafa itace hana tallace tallace a gefen titunan da ke fadin jahar. Brinin Lagos ya kasance mai jan hankalin 'yan ci rani musamman daga arewacin Najeriya, kuma akasarin masu tallar matasa ne daga arewacin kasar.

Tun daga misalin karfe biyar na asuba zaka ga wadannan masu tallace tallace na sayar da kayayyaki irin su cingam ko alawa ga masu tafiya a cikin mota, wasu lokuta harda lemun kwalba da sauran kayayyaki makamantan su.

Sai dai gwamnati ta bayyana irin wadannan tallace tallace da ake yi a matsayin dalilin da yake haifar da cinkoson motoci wanda ke kawo cikas ga masu tafiye tafiye a kan ababen hawa tare kuma da barazanar tsaro ga al'umar jahar, abinda ya sa aka kaddamar da wannan doka kenan.

A cewar masu tallace tallacen, wannan doka bata yi masu dadi ba, domin kuwa da tallar suka dogara, nan suke samun kudin abinci, sutura, da ciyar da wadanda ke karkashin su. Dan haka a cewar su, wannan ba adalci a bane, dan haka suna roko a yi masu alfarma domin gari baya ci gaba idan babu baki.

Ta gefen gwamnati kuma, hukumonin sun bayyana cewar sun dauki wannan mataki ne a yunkurin samar da tsaro da kuma kawar da 'yan zauna gari banza, a yanzu haka rahotanni sun nuna cewar gwamnatin ta fara kama masu talace tallacen.

Ga rahoton Babangida Jibrin 02' 53"