Kakakin mayakan ruwan Najeriya, Navy Commodore Ayo Vaughan ya shaida wa VOA Hausa cewa su wadannan sojin ruwan bogi da aka gano na da hedikwatarsu a shiyyar kudu maso kudancin Najeriya ne, inda suke gudanar da haramtacciyar hada hadarsu.
Wasu Mata Sojin Gona
Za ka gansu tsaf tsaf cikin kakin sojin ruwa makale da lambobin girma da ababen dai da ke jikin kakin sojin ruwan har ma wani babban ofis suke da shi da adireshin yanar gizo, har ma sai da form na daukar aiki su ke yi inda suke damfarar jama'a.
Wasu Mata Sojin Gona
Wannan rundunar mayakan na bogi na nuna izza da isa yayin da a wani lokaci suke cin zalin jama'a a matsayin su sojoji ne.
Wasu Mata Sojin Gona
Saboda haka Hedkwatar mayakan Ruwan Najeriya ta ce za ta dau mataki mai tsanani akansu kana ta nemi jama'a da su yi takatsantsan, sannan su kai rahoton duk wadanda ba su yarda da take-takensu ba.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina: