Yayin da ake dawowa da gawar daya daga cikin sojojin a jiharsa ta Florida a wannan mako, Mattis yace rundunar zata fidda sabuwar sanarwa da zarar ta samu bayanai a cikin lokaci.
Yace ana bincike a kan rashi da muka yina dakarunmu. Mu a ma’aikatar tsaron muna son mu san abin da muke fadi kafin mu bayyanar dasu, kuma a wannan lokaci bamu da cikkan bayanai a kan wannan batu. Zamu fitar da bayanai cikin gaggawa kamar yanda zasu shigo mana saboda muna alfahari da dakarunmu. Kamar yanda kuka sani, muna gudanar da bincike duk lokacin da aka kashe mana sojoji.
An kashe sojojin ne a farkon wannan wata a wani kwantan bauna da mayakan jihadin Isama suka yiwa dakarun Amurka da na Nijer a wani fada da yyi sanadiyar kashe sojojin Nijer guda hudu.
Sanata John McCain mai yawan sukar lamirin shugaba Trump ya yi barazanar shigar neman izinin sammaci na Karin bayani a kan wannan hari.