BAUCHI, NIGERIA - Manya daga cikin mutanen da suka sauya shekar daga jam’iyyar APC zuwa PDP, sun hada har da tsohon mataimakin gwamna a jam’iyyar APC, Alhaji Abdu Sule, kakakin majalisar dokokin Jihar Bauchi, Yakubu Y. Suleman da kuma Honarabul Faruk Mutafa, wanda ya yi takarar kujerar gwamna karkashin jam’iyyar APC, wanda shi ya gabatar da mutanen da suka yi sauyin shekar.
Jiga-jigan ‘Ya’yan Babban Jam’iyar Adawa Ta PDP Sun Kai Wata Gagarumar Ziyara Jihar Bauchi
Babban bako a wajen taron kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben badi, Alhaji Atiku Abubakar, ya taya al’ummar jihar Bauchi murna kan irin ci gaban da aka samu a jihar.
Jiga-jigan ‘Ya’yan Babban Jam’iyar Adawa Ta PDP Sun Kai Wata Gagarumar Ziyara Jihar Bauchi
Jiga-jigan ‘Ya’yan Babban Jam’iyar Adawa Ta PDP Sun Kai Wata Gagarumar Ziyara Jihar Bauchi
A nasa jawabin mai masaukin baki, gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammed, Kauran Bauchi, ya shaida cewa siyasa a arewa daga Bauchi aka fara, kuma Bauchi garin Wazirin na Adamawa ne.
Jiga-jigan ‘Ya’yan Babban Jam’iyar Adawa Ta PDP Sun Kai Wata Gagarumar Ziyara Jihar Bauchi
Wadanda suka halarci taron na Bauchi sun hada da Sule Lamido, Ibarahim Hassan Dankwambo, Bukola Saraki, Sanata Dino Melaye, da sauran kusoshin jam’iyar PDP na shiyyar Arewa Maso Gabas da kuma sassan kasa baki daya.
Saurari cikakken rahoto daga Abdulwahab Muhammad:
Your browser doesn’t support HTML5
Jiga-jigan ‘Ya’yan Babban Jam’iyar Adawa Ta PDP Sun Kai Wata Gagarumar Ziyara Jihar Bauchi .mp3