Shirin na wannan makon, zai kawo muku kashi na bakwai kuma na karshe na ci gaba da tattaunawa da shugabannin kungiyoyin manoma mata da maza a Najeriya wanda suka koka cewa tsohuwar gwamnatin Buhari ta ba da umarnin a basu tallafi domin su yi noma har su ciyar da kasa sannan a sayar wa wasu kasashen duniya, amma tallafin bai kai gare su ba.
Shugabannin sun bayyana irin matakan da suke dauka wajen taimakawa 'yan kungiyarsu.
Saurari shirin cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5
NOMA TUSHEN ARZIKI: Tinubu Ya Ce Zai Ci gaba Da Samarwa Manoma Tallafi Da Dabarun Inganta Noma 7'05.mp3