Ina zuwa kasuwa domin sana’ar sayar da ganda a lokutan da bana zuwa makaranta ko lokacin da aka tafi yajin aiki a makaranta da zumar zama mai dogaro da kai
Matashiya A’isha Ma’aruf, ta bayyana haka ne a yayin da take zantawa da DandalinVOA, inda ta bayyana tana taimakawa mahifiyarta ne a wsu lokuta inda take zuwa kasuwar ‘yan ganda domin ta saro ganda.
Ta kuma ce tana kaiwa kasuwar sabon gari don sayarwa mata masu abincin gida ko na kasuwa , tana kuma yin sana’ar ne domin dogaro da kai kafin lokacin da zata kammala karatunta na lauya.
Aisha ta ce a halin yanzu basa samun riba sosai sakamakon tsada da gandar ta yi koda shike sukan sami ‘yar karamar riba a gandra rakumi.
Daga karshe ta kara da cewa sana’ar hannu wajibi ce ga diya mace da ma dukkan matasa masu tasowa.
Your browser doesn’t support HTML5
Nema Ilimi Bai Hana Sana'a - Inji A'isha Mai Karatun Lauya