NIAMEY, NIGER - A cikin shirin na wannan makon mun nufi Damagaram a Jamhuriyar Nijar don duba halin da ake ciki a makarantar firamari ta makafi da ake kira birnin Garçon wacce aka kafa a shekarar 2000.
Makarantar Yara Makafi A Jamhuriyar Nijar
Shekaru sama da 20 bayan bude wannan makaranta ana iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu domin dimbin ma’aikata makafi da ake damawa da su a yau a fannoni daban-daban sun bi ta wannan makaranta.
Sai dai kuma bayanai na nunin a yau al’amuran karatu ba sa tafiya kamar yadda ya dace sakamakon tarin matsalolin da ake fuskanta kamar yadda Darektan makarantar ta birnin Garçon Ibrahim Moustapha Titi ya bayyana a hirarsu da Muryar Amurka.
Saurari cikakken shirin daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5
NAKASA BA KASA BA: Halin Da Ake Ciki A Makarantar Firamari Ta Makafi “Garçon” A Nijar, Nuwamba 3, 2022.mp3