Mutane 5 Sun Yiwa 'Yar Shekaru 13 Fyade

An gurfanar da wasu mutane biyar(5) a kotu, ana zargin su da yiwa wata ‘yar shekaru goma sha uku (13) fyade wanda ya zama juna biyu. Mutanen sune Amadu Mairake, dan shekaru 60, Samaila Hamza,30, Hassan Surajo, 40, Sani Abdullahi,30, da Hassan Ila dan shekaru 40.

A wani labari hukumar ‘yan Sanda ta ce wadanda ake tuhumar mazauna kauyen Borin-Dawa ne a karamar hukumar Malumfashi dake jahar Katsina.

Mahaifin yarinyar Abdulmalik Nuhu, ne da kanshi ya kai rahoton ga ‘yan Sanda.

A lokacin sauraren karar mai gabatar da karar, Mr. Hashimu Musa , ya fada wa kotu cewa laifgiun da ake tuhumar su da shi ya sabawa sashe na 283, na dokar kasa.

Alkalin kotun Hajiya Nafisah Bagiwa, ta ce za’a tura shariar zuwa ma’aikatar sharia dan neman shawara, an dage karart har sai zuwa 28, ga Oktoba nan da muke ciki.