Kai tsaye Ri ya danganta kalaman shugaban na Amurka Donald Trump a ranar Asabar da ya dora a shafin sada zumunta da wannan barazana. Da yake maida martani a kan jawabin Ri a wurin babban taron MDD tun da farko, Trump ya rubuta cewar, yanzu y agama sauraren ministan harkokin Korea ta Arewa a MDD. Idan ya maimaita kalaman mutumin nan mai kananan rokoki, zai yi kaca kaca dasu.
A yau Litinin ministan harkokin wajen Korea ta Arewa ya maida martani a kan wannan batu.
Yace ganin wadannan kalaman sun fito daga bakin wanda ke shugabancin Amurka, ko shakka babu yaki ne aka ayyana, inji Ri yana fadawa manema labarai a otal din da yake zaune a birnin New York. Yace kasashen da suke halartan taron MDD da ma duniya baki daya su tuna da cewar Amurka ce ta fara kada gangar yaki a kan kasarsa.
Ministan na Korea ta Arewa ya kara da cewar, zasu samu hurumin daukar matakan mayar da martani, ciki har da harbe jiragen yakin Amurka koda kuwa basu karaso a sararin samaniyar kasarsa ba a wani kashedi da yayi.