‘Yan Najeriya mazauna Nijer sun tofa albarkacinsu a game da sunayen mutanen da shugaba Muhammadu Buhari ya aikawa majalisar dattawa domin tantancewa kafin a nada su ministoci a sabuwar gwamnatin da yake shirin kafawa.
Kusan ana iya cewa wannan magana ta jerin sunayen da shugaba buhari ya aikawa majalisar dattawan Najeriya domin tantancewa kafin a basu mikamin minista ita ce maganar dake daukar hankalin ‘yan Najeriya mazauna Nijer a yanzu haka. Wadanda wadanda wakilin sashin Hausa ya tunutuba sun bayyana gamsuwa da zabin na Mahammadu Buhari.
A dangane da rashin saka matasa a shirin kafa sabuwar gwamnatin ta Muhammadu buhari ‘yan Najeriya mazaunan Nijer na ganin lokacin ba matasa mukaman gwamnatin tarayya bai yi ba.
Ga wadanda majalisar dattawa za ta amincewa shigarsu cikin sabuwar gwamnatin da APC ke shirin kafawa watanni kusan 6 bayan lashe zabe ‘yan Najeriya mazauna Nijer na gargadinsu da su kasance masu rikon amana tare da maida dukkan wasu bambance bambance share daya.
Saurari Cikakken Rahoton.