Matan Karkara na Kokawa Kan Rashin Kulawa Daga Hukumomi

Batun habaka tattalin arzikin matan karkara ta hanyan bunkasa Noma, na daga cikin hanyoyin cimma sabon shirin muradun ci gaba mai dorewa da kasashen duniya suka san yawa hannu ciki kuwa harda Najeriya, a yayi taron koli na Majalisar Dinkin Duniya da aka kamala cikin watan jiya a birnin New York na kasar Amurka.

Sai dai mata mazauna karkara a jahar Kano, dake sana’ar noma da sauran sanao’in dogaro da kai na kokawa kan rashin kulawa daga hukumomi.

Hajiya Talatu Salamatu Bashir, ta Bankin {Women Development Bank}wanda ke bada rancen bunkasa sanao’in mata a Kano, ta ce tilas ne hukuma ta tallafawa mata masammam ma ma zauna karkara.

Tun a shekara ta 2013, ne Babban Bankin Najeriya, ya kebe kudi fiye da Naira biliyan dari biyu domin bada tallafin rance ga kananan manoma a kasar, amma har yanzu jahohi da dama a Najeriya, basu kai ga cin gajiyar kudaden ba ciki harda jahar Kano.