Mata Masu Sana’ar Daukan Hoto Na Fuskantar Kalubale - Ummu Ayman

Ummu Ayman – matashiya mai sana’ar kwaliya wato “make-up” da daukar hoto ta ce tun tana makaranta ne ta fara sana’ar daukar hoto.

A cewarta, a lokacin tana makaranta, ba ta mai da shi sana’a sosai ba,inda ta ce, ta na yi ne kawai domin sha’awa.

Amma bayan da ta kammala karatun digirinta, sai ta lura cewa sana’a ce mai kyau.

Kasancewar ta ‘ya mace, Ummu ta bayyana irin rashin hadin kai da ake nunawa mata akan daukar hoto, musamman ma a wuraren biki ko duk wani wajen taron jama’a, tana mai jaddada cewa ba’a ba su gudunmuwar da ta dace domin gudanar da sana’arsu yadda ya kamata.

Ta ce, wannan matsala ta fi fitowa daga wajen 'yan uwansu mata, inda a mafi yawan lokutan akan yi musu kallon raini, maimakon a mara musu baya wajen jajircewarsu na ganin sun dogara da kansu.

Ummu Ayman ta ce, baya ga daukar hoto tana ayyukan yin kwaliya ga amare ko 'yan mata da duk macen da take bukata sannan ta dauki hoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Ummu Ayman: Wata Matashiya Mai Sana'ar Kwalliya Da Daukar Hoto 4'08"