A wani al'amari mai kama da martani, bayan da aka kai harin bam wanda ya kashe mutane hudu da su ka hada da 'yan kasar Vietnam uku da wani dan Masar, kasar Masar ta kai samame har sau uku a lokaci guda, inda ta karkashe 'yan bindiga 40
WASHINGTON D.C. —
Hukumomin Masar sun ce jami'an tsaron kasar sun hallaka wasu da ake zargin 'yan bindiga ne su 40 a wasu samame uku da aka kai a lokaci guda jiya Asabar a Giza da kuma arewacin Sinai.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da wasu 'yan yawon bude ido 'yan kasar Vietnam su uku da kuma wani dan kasar Masar mai masu jagora su ka mutu bayan da bam ya bararraka motar bus dinsu daura da Giza.
Wasu 'yan Vietnam din wajen 11 da ke cikin motar da direbansu dan kasar ta Masar sun samu raunuka sanadiyyar tashin wannan bam din da aka dana a gefen hanya.
Ministan Harkokin Cikin Gidan Masar dai bai fayyace ko 'yan bindigar da aka kashe jiya Asabar din na da alaka da harin da aka kai ma motar ta bus.