Ranar litinin da ta gabata ne wata kotu ta yanke ma wani mutum mai suna Mathew Oluyede dan shekaru 51 hukuncin zama gidan yari bisa zarginsa da aikat laifin cin zarafin wasu kananan yara 'yan makaranata su hudu.
Mai shari'a Taiwo Ajibade wanda ya ki amincewa da bada belin malamin, ya bada umurnin aika mai laifin gidan yari, ya kuma kara da cewa zai ci gaba da kasancewa a gidan yarin har sai ranar da aka gama sauraron shari'ar.
Alkalin ya bada umurnin cewa a sake buga wani kwafi na takardun laifin da mutumin ya aikata a aikama sashen kula da shari'a koken jama'a domin neman karin shawara kan irin hukuncin da ya cancanci a yanke masa.
A yayin da yake bada shaida, dan sanda mai gabatar da kara mai mukamin saja Akinwale Oriyomi, ya bayyanawa kotu cewar malamin ya aikata laifin tsakanin 19 ga watan goma zuwa 20 ga watan ne a wani kauye da ake kira Ayetoro - Ekiti.
Mai gabatar da karar ya bayyana wa kotun cewar ana zargin malamin da cin zarafin yara guda hudu wadanda shekarun su tsakanin 2 da 9 ne.
A cewar alkalin, laifin da malamin ya aikata sabawa sashi na 218 na aikata muggan laifuka a jahar.