Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Rabiu Kwankwaso ya zabi Fasto Bishop Isaac Idahosa a matsayin mataimakinsa a zaben 2023.
WASHINGTON —
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Rabiu Kwankwaso ya zabi Fasto Bishop Isaac Idahosa a matsayin mataimakinsa a zaben 2023.
Presidential candidate of the New Nigeria Peoples Party, NNPP, Rabiu Kwankwaso
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Alhamis da cewa “Mataimakin Shugaban Kasarmu Fasto Bishop Isaac Idahosa daga jihar Edo.”
Shafin Twiiter Kwankwaso
Pastor Bishop Isaac Idahosa
Bishop Idahosa, wanda ya fito daga jihar Edo shi ne babban Fasto na God First Ministry, da aka fi sani da Illumination Assembly.
Cocin na da hedikwata ne a Lekki, jihar Legas.