Gwamnatin jahar Yobe ta bayyana kashi 38% cikin dari na sakamakon jarabawar kammala makarantar sakandire NECO a jahar a matsayin koma bayan da abinda baza'a amince da ita ba.
Mujallar Vanguard ta bayyana cewar kwamishinan ilimin jahar Alhaji Mohammed Lamin ya bayyana hakan a yau laraba yayin da ya amshi jan ragamar ayyukan ma'aikatar ilimi a Damataru.
Kwamishinan wanda ya bayyana kudirin gwamnatin jahar na canza yadda ake gudanar da harkokin ilimin, ya yi kira ga malaman makarantun jahar da su zage damtse wajan aiwatar da ayyukan su domin inganta ilimin daliban jahar baki daya.
Ya kara da cewar gwamnatin Ibrahim Gaidan mai mulki yanzu, zata samar da isassun kayan aikin da ake bukata a duk fadin jahar domin ciyar da ilimin daliban jahar gaba.
Daga karshe kwamishinan ya bayyana kashi 50% cikin dari a matsayin wanda kwzon da gwamnatin jahar zata iya amincewa da shi a makarantun gwamnati, ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a harkokin ilimi wadanda suka hada da malaman makarantu, da shugabannin makarantu, da iyaye da na al'uma baki daya su hada hannu da gwamnati domin ciyar da ilimi gaba a jahar.