Hukumar EFCC ce ta gabatar da kara a gaban kotun Chuka Obiozo inda ta gabatar da sheidu da suka tabbatar an sayi gidajen ne da kudaden gwamnati.
Gidajen suna tsibirin Banana Island ne, wata unguwa ta masu hannu da shuni a jihar Legas.
A ranar 19 ga watan Yulin bana ne dai ta gabatar da sheidun da ya sa Alkali Obiozo yanke hukumcin kwace gidajen. Amma kafin ya yi hakan ya umarci hukumar EFCC ta buga cigiyar wadanda suka mallaki gidajen cikin jaridu. Idan babu wanda ya fito ya nuna gidajen nashi ne to kotun zata baiwa gwamnati gidajen.
Jiya da alkalin ya zauna bayan da wa'adin ya cika babu wanda ya fito ya nuna gidajen mallakarsa ne.
Lauyan hukumar EFCC Ansale Ozioku ya shaidawa kotu cewa sakamakon gazawar wani ya fito ya bayyana kansa a matsayin wanda ya mallaki gidajen ya zama wajibi bisa tsarin doka a mallakawa gwamnati gidajen.
Shehun Malami Muhammad Lawal Yusufari ya bayyana abun da hukumcin ke nufi. Yace idan ana zargin wani da mallakar wasu kadarorin da aka saya da kudin gwamnati hukuma nada hurumin ta kai kara kotu domin a mallakawa gwamnati kadarorin.
Hukumar EFCC ta gabatar da sheidun da suka nuna yadda aka yi anfani da wasu kamfanoni da bankuna aka wawure kudin gwamnati. Wasu jami'an bankuna sun tabbatar cewa lallai sun karbo wasu kudade daga hannun ministar a gidanta dake Abuja a shekarar 2013.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5
Kotu Ta Mallakawa Gwamnatin Najeriya Wasu Gidajen Mrs Madueke dake Legas - 3' 33"