Hukumar kwallon kafar Najeriya ta NFF, ta ba da tabbacin cewa za ta gana da kungiyoyin kwallon kafa na Premier League a Najeriya, domin a tabbatar an saki ‘yan wasa akan kari kafin karawar da Super Eagles za ta yi da ‘yan wasan Rwanda a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afrika da za a yi a shekara mai zuwa.
Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da kocin ‘yan wasan Najeriya na ‘yan kasa da shekaru 23, Samson Siasia, ya ke kokarin shima ya hada kan ‘yan wasan da za su kara a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar afrika ta ‘yan kasa da shekaru 23 a Senegal.
Hukumar ta NFF, na kokari ta hadu da kungiyoyin ne domin a kaucewa aukuwar abinda ya faru a baya kafin gasar da za a yi a farkon shekara mai zuwa a cewar wata majiya da ta gana shafin wasanni nan a yanar gizo da ake kira Completesportsnigeria.com.
Zai dai a buga gasar ta cin kofin nahiyar Afrika ne a tsakanin 16 ga watan Jainairu zuwa 6 ga watan Fabrairun shekara mai zuwa a biranen Kigali da Gisenyi da Bature da ke kasar Rwanda.
Ana sa ran kakar wasan gasar Premier ta Najeriya za ta kare ne a wannan wata na Nuwamba inda za a dawo a watan Janairu domin fara wata sabuwar kakar wasa.