Karya Doka A Thailand jawo ma kai Masifa Ce

Thai marine police

A yau Talata Jaridar New York Times, ta ce ba a buga takwarar jaridar a kasar Thailand ba, saboda ta dauko wani labari kan rashin lafiyar Sarkin kasar tare da dasa alamar tambaya kan makomar masauratar.

Kasar ta Thailand dai na da dokoki masu tsauri da suka haramta sukar masarautar, inda aka tanadi hukunci zaman gidan yari na tsawon shekaru 15 ga duk wanda ya karya dokar.

An dai samu karin take wannan doka, tun bayan da sojin kasar suka yi juyin mulki a bara.

A wata sanarwa da kamfanin jaridar ya fitar ta hanyar email, mai buga takwarar jaridar a Thailand ya bayyana cewa, ya ki amincewa da fitar da ita ne, saboda labarin rashin lafiyar sarkin kasar wanda aka buga a shafin farko, abu ne da ake dari-dari da shi.

Sai dai shugabannin kamfanin jaridar New York Times da ke nan Amurka sun ce, wannan mataki ne da mai buga jaridar ya dauka na gashin kansa, wanda ba sa goyon baya.