Rashin daidaito da yin anfani da matsayi a wuraren ayyuka na taka rawa musamman wajan dakushe ra'ayin mata wajan sa hannu domin gina al'uma da ciyar da kasa gaba.
A yau dandaloin VOA ya zanta da wata matashiya 'yar shekaru 27, mai suna Khadija Ibrahim wadda ta bayyana irin kalubalen da ta fuskanta a tsakanin ta da nagaba da ita a ofisoshin da ta yi aiki.
A cewar matashiyar, na farko dai bayan ta kammala karatun gaba da sakandire, ta sami aki da wata makaranta inda take koyarwa, sai dai bata dade ba domin ta fuskanci takura musamman ta yadda shugaban makarantar ya nuna mata ra'ayin sa na bukatar ta rika yi masa rakiya. Ta kara da cewar hakan ne yayi sanadiyyar sa ta cikin damuwa kwarai wanda daga karshe ta ji baza ta iya ci gaba da aikin ba.
Matashiyar ta ce "na bar aikin saboda banaso ya bata min rayuwa, na sake samun wani aikin wanda da farko na yi tunanin hakan bazata kasance da ba, kwatsam sai wata rana mai kula da sashin da nake aiki ya budi baki ya fara nuna mani wasu irin bakin halayen da basu kamata ba."
Daga karshe malama Khadija Ibrahim ta nuna ra'ayin ta na sake komawa makaranta domin karo ilimi domin kaucema irin wannan kalubale.
Saurari cikakken rahoton;