Kadan Daga Nollywood

A sakamakon labarin da ya fito na haihuwar ‘Yan tagwayen jarumar nan Nadia Buari, da dama sun zargi cewar tsohon saurayinta Jim Iyke, ne uban yaran.

Amma rahotanni daga kasar Ghana, sunce Iyke, wanda ya taba nemanta da aure a wani shirinsa na talabijin wanda ake tsara shi bisa zahirin abinda ke faruwa, yace ba shi ne uban yaran ba.

Mai gabatar da shirin Late Nite celebrity show TV Vanessa Gyan, ta bayyana cewa jarumar ta haihu ne a wani Asibiti dake Atlanta, da taimakon mahaifiyarta da dan uwanta wanda daga baya saurayinta wanda take niyyar aure ya zo.

Ta kara da cewar Jim iyke, ba shine mahaifin ‘yan biyun ba, domin a yanzu haka jarumar na da baikon uban tagwayen data haifa.

Your browser doesn’t support HTML5

Kadan Daga Nollywood