Asibitin Glenfield dake birin Leicester ya fada a jiya Laraba cewar jaririya mai suna Vanellope Hope Wilkins da aka haifa a karshen watan Nuwamba, zuciyarta na girma ne a wajen jikinta, wani lamari na ba saban ba.
An yi mata tiyata na farko inda aka mayar da zuciyarta a cikin jikinta bayan awa daya da haifuwarta.
Dr. Nick Moore yace jaririyar tana kwance a sashen kula na musamman da aka kebe na jarirai.
Jarirai takwas kadai a cikin kowadanne jarirai miliyon ne ake haifa da zuciya a wajen jikinsu. Kuma galibin wadanda ake haifuwa da wannan matsala ne suke mutuwa cikin kwanaki uku da haifuwar su.
Likitoci masana aikin zuciya sun ce basu da masaniya a kan wani jaririn dake fama da wannan matsala ya rayu ko ya samu lafiya bayan tiyata a kasar Britanniya. Amma jarirai masu wannan matsala da dama sun rayu a Amurka bayan an yi musu tiyata ciki har da Audrina Cardenas wacce aka haifa a jihar Texas a shekarar 2012.