Jam'iyar APC ta Koka da Gwamnatin Jahar Naija ta PDP
Gwamna Ma'azu Babangida Aliyu na jahar Naija.
Jam'iyar APC na zargin gwamnatin jahar Naija ta PDP da kwarzaba, da cin zarafi da kuma bita da kulli
WASHINGTON, DC —
Babbar jam'iyar hamayya ta APC a Najeriya, ta gabatar da kwararan shaidun da ke nuna cewa gwamnatin jahar Naija ta PDP na bin 'yan APC a jahar, ta na kafa musu k'ahon zuk'a, ta na kwarzabar su kuma ta na yi musu bita da kulli.
Wakilin Sashen Hausa a jahar Naija Mustapha Nasiru Batsari ya bugi jaki, ya bugi taiki, ya hada rahoto akan wannan matsala kamar haka:
Your browser doesn’t support HTML5
Rikicin PDP da APC a jahar Naija.- 3':21"
Masu yin wannan zargi sun ce ba komi ba ne ya jawo wannan cin mutunci illa kawai don sun bar jam'iyar PDP sun koma APC.