Jami'an Tsaro A Sri Lanka Na Ci Gaba Da Yaki Da 'Yan Ta'adda

Jami'an tsaro a Sri Lanka

An gano wata mace da mummunar rauni tare da wani yaro a yau Asabar a lokain da gyaran wata gida a Sri Lanka inda jami’an tsaro suka yi musayar wuta da wani gungun ‘yan bindiga a Kalmunai dake yankin gabashin kasar. An kwantar da matar da yaron a asibiti.

Mai magana da yawun ma’aikatar sojin kasar yace an gano gawarwaki 15 ciki har da kananan yara shida a ciki da wajen gidan, inda aka yi musayar wutar da ma abubuwan fashewa, lamarin da ya faru a jiya Juma’a.

‘Yan sanda sun ce akwai yiwuwar abubuwar fashewar da suka tashi, ayyuka ne na masu kai harin kunar bakin wake.

Rundunar sojin kasar ta samu abubuwan fashewa 15, da rigar da ‘yan kungiyar IS ke amfani da ita, da jirage mara matuka a cewar wata jaridar kasar Sri Lanka The Daily Mirror. An kuma samu komputar tafi da gidanka da babbar mota a gidan.

Shugabannin mujami’ar Katolika sun soke duk wasu tarukansu na gobe Lahadi a fadin kasar, yayin da jami’ai suka ce akwai yiwuwar karin hare hare a wannan tsibiri, biyo bayan kusan mako daya da kai mummunar harin nan na ranar bukin Easter a ranar Lahadi ya gabata da masu kai harin kunar bakin wake suka tada bama bamai a mujami’u da otal otal, lamarin da ake zargi masu tsaurin ra’ayin Islama da aikatawa.