PNDS Tarayya Ta Musanta Zargin Hannun Tsohon Shugaba Issouhou Mahamadou A Juyin Mulki

 Boubacar Sabo, sakataren harakokin zaben jam’iyar PNDS Tarayya ta Nijar

Boubacar Sabo, sakataren harakokin zaben jam’iyar PNDS Tarayya ta Nijar

Jam’yar PNDS Tarayya madugar kawancen jam’iyun hambarariyar gwamnatin Nijar ta musanta zargin hannun tsohon Shugaban kasa Issouhou Mahamadou, a juyin mulkin da soja suka yi wa Mohamed Bazoum a ranar Larabar ta gabata.

NIAMEY, NIGER - A wata sanarwar da ta fitar a ranar Asabar uwar jam’iyar ta ce masu neman maida hannun agogo baya a yunkurin dorewar dimokradiya ne ke wannan ikirari da nufin dakile shirin sake mayar da shugaba Bazoum kan kujerar mulki.

Wannan bayani ne daga sakataren harakokin zaben jam’iyar PNDS Boubacar Sabo a lokacin da yake tanttaunawa da wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma a birnin Yamai.

Ga cikakken rahoto yadda hirar tasu ta kaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Jam'iyar PNDS Ta Musanta Zargin Hannun Tsohon Shugaba Issouhou Mahamadou A Juyin Mulki .MP3