Mutane da dama sun makale a tashar jirgin ruwa ta Sicilian dake Catania a cikin jirgin ruwan Diciotti, tun cikin daren Litinin, saboda gwamnatin Italiya taki yarda a saukesu, har sai kasashe mambobin Kugniyar Tarayyar Turan sun amince su karbi wasu a cikin mutanen.
Luigi Di Maio shine Mataimakin Frai Ministan Italiya yace shi da sauran jami’iyyun siyasar kasar ba zasu yarda su bada euro biliyon 20 ga Kungiyar Tarayyar Turai a duk shekara. Yace zasu rike wani bangare na kudin, har sai an tabbatar da wani kasafi da zai sa ido a kan biliyon 20 na Tarayyar Turan.
Nan da nan helkwatan Kungiyar tarayyar Turai dake Brussel ta maida martani a kan kalaman Di Maio, ta bakin mai Magana da yawun hukumar zantarwar Kungiyar Alexander Winterstein,
Yace kada fa wannan magana ta kaimu ga dorawa juna laifi. Kuma mun amince kalamai marasa kyau da barazana ba zasu kai mu ga warware matsala ba. Kungiyar Tarayyar Turai kungiya ce mai dokoki kuma tana gudanar da ayyukanta a kan dokokinta amma ba barazana ba. Don haka zamu nemi kowane bangare ya hada hannu wurin shawo kan wannan matsala domin taimakawa wadannan mutane kai hade.