A yau Laraba Jami’an tsaro, sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga zanga a bakin ofishin jakadancin Amurka da ke Bagadaza, zanga zangar da mayakan da ke samun goyon bayan Iran ke gudanarwa, wacce ta shiga yini na biyu a yau.
Zanga Zanga A Birnin Bagadaza
Da dama daga cikin masu zanga zangar sun kafa tantuna a bakin ofishin inda suka kwana a waje, bayan da a jiya Talata suka yi nasarar ketare shingen da ke bakin ofishin, suka yi ta cinna wuta.
Zanga Zanga A Birnin Bagadaza
Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Talata, ya ce zai rike Iran akan duk wata barna da ta faru ko wani rauni da aka ji wa wani a ofishin.
Amma ya kuma yabawa jami’an tsaron Amurka da suka kare ofishin jakadancin.
“Ina ga sun yi kokari, dakarunmu sun yi abin a zo a gani, kuma sun isa wurin cikin dan kankanin lokaci.” Trump ya ce.
Zanga Zanga A Birnin Bagadaza
Sai dai yayin da yake ganawa da manema labarai da yammacin jiya Talata, Trump ya kore yiwuwar fadawa Iran da yaki.