Hukuncin Daurin Rai Da Rai Akan Laifin Fyade a Jahar Kano

.

Gwamnatin jahar Kano, ta ce yanzu duk wanda aka kama da laifin yin fyade zai kwashe shekaru 14, a gidan yari a matsayin hukunci mafi karanci ko kuma ya karashe yaruwar sa a gidan yari ma'ana daurin rai da rai.

Babban Lauyan Gwamnati na jahar ta Kano Mukthar Daneji, ne ya furta haka a wurin taron kungiyar "Justice For All" inda ya kara da cewa da hukunci fyade a jahar shekara 1, ko 2, ko kuma tara.amma hukunci na yanzu babu zabin tara.

Ya na mai cewa yanzu iyaye da dama na fidda kunya suna kawo karan duk wanda ya yiwa 'ya'yan su fiyde, ya ce wannan bai rasa nasaba da kara wayar masu da kai da ake yi ba.

Shi kuwa babban daraktan kungiyar ta "Justice For All" Bob Arnot, ya ce kungiyar sa tana aiki hannu da hannu da hukumomin 'yan Sanda da ma'aikatan sharia domin samarda da karin tsaro da tabbatar da cewa sharia tayi aikin ta.

Ya kara da cewa kungiyar sa na taimakawa wadanda suka kamu da cutar HIV da kuma wadanda aka ci zarafinsu.