Yemi Mobolade, dan asalin Najeriya, ya yi nasarar lashe zaben kujerar magajin gari, inda zai dare mukamin a Colorado Springs, birni na biyu mafi girma a jihar Colorado ta kasar Amurka da ke da tarihin kasancewa tungar masu ra'ayin rikau. Shi ne kuma bakar fata na farko a tarihin birnin da aka taba zaba Magajin Gari.
Yemi Mobolade Sabon Magajin Garin Birnin Colorado Springs Da Ke Jihar Colorado tare da Ma'aikacin Sashen Hausa, Haruna Shehu
A hirarsa da Haruna Shehu Marabar Jos gabanin rantsar da shi, Yemi Mobolade ya fadi abin da nasarar da ya samu ta ke nunawa a duniya.
Saurari hirarsu:
Your browser doesn’t support HTML5
Hira Da Yemi Mobolade, Sabon Magajin Garin Birnin Colorado Springs Da Ke Jihar Colorado