Duk da mummunan koma bayan da Hizbullahi ta samu a makonnin baya-bayan nan, shugabanta na riko Naim Kassem ya bayyana a cikin sanarwar da aka yada ta kafar talabijin cewar idan har Isra’ila ta yanke shawarar kaddamar da yaki ta kasa, a shirye mayakan kungiyar suke, inda yace an riga an maye gurbin kwamandojin da ta hallaka.

Lebanon 30 Satumba 2024. (Foto: Jim Urquhart/REUTERS)
Kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ba za ta bata lokaci ba wajen zabin mutumin da zai gaji jagoranta da aka hallaka Hassan Nasrallah sannan zata cigaba da yakar Isra’ila, a cewar mataimakin shugaban kungiyar da Iran ke marawa baya Naim Qassem a yau Litinin.

Ya yi bayanin ne a jawabin da aka yada ta kafar talabijin, karon farko ke nan da wani jami’in Hezbullah ya bayyana tun bayan kisan da wani harin Isra’ila ya yiwa Nasrallah a yankin kudancin babban birnin Lebanon a Juma’ar da ta gabata.
Hare-haren Isra’ila ta sama sun hallaka Nasrallah tare da wasu manyan kwamandoji da jami’ansa 6 a kwanaki 10 da suka gabata, kuma ta kai hari kan wuraren da rundunar sojin ta bayyana da mallakin Hezbullah ne a sassan Lebanon da dama.
Hassan Nasrallah
Cikin makwani 2 da suka gabata an hallaka fiye da mutane dubu a Lebanon, kusan 1 bisa 4 mata da kananan yara, a cewar ma’aikatar lafiyar kasar.
-Reuters