A jiya Lahadi mujallara Mirror ta wallafa rahoton wani matashi matafiyi mai shekaru 24, daga Birnin Lisbon zuwa Dublin ya rasa ransa a cikin jirgin sama yayin da jirgin ke tsakar tafiya a sararin sama.
Ma'aikatanb jirgin saman sun bayyana cewar matashin dan kasar Brazil ne wand ke makaranta a tsibirin Irelan ya gangantsara ma pasinjan da ya zauna kusa da shi cizo sa'annan jama'a suka rike shi.
'Yan sandan Irish sun bada sanarwar cewa saida aka kaiga karkata akalar jirgin zuwa wani filin jirgi maisuna Cork a bayan jam'a sun yi kokarin hana shi wanda daga karshe kawai sai ya fara suma.
Wani likita da wata ma'aikaciyar jiyya dake cikin jirgin sunyi kokarin ba matashin taimakon agajin gaggawa amma da misalin karfe shidda da minti arba'ain na yamma 6:40pm ya cev ga garin ku nan.
'Yan sanda sun cafke wata mata mai shekaru 44 a cikin jirgin wadda take dauke da sinadarin amphetamin wadda aka yi zargin tafiyar su guda da matashin.
Wani ganau a cikin jirgin ya bayyana irin karar da matashin ya fara, wadda yace bai taba jin irinta a rayuwarsa ba kuma ya kara da cewa baya fatan ya sake jin irin wannan karar.