Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya kaddamar da gidaje 500 da gwamnatinsa ta gina a Nguro-Soye dake karamar hukumar Bama a jihar Borno don tsugunar da mutanen da rikicin Boko Haram ya kora a yankin.
Lokacin Rabon Kaya Ga Wadanda Suka Samu Tallafin Sabbin Gidaje 500 A Garin Nguro-Soye
Gidajen suna da abubuwan bukata irinsu makarantu, cibiyar kula da lafiya, famfunan ruwa da sauran abubuwan bukata.
Garuruwan da aka tsugunar da su, sune Burari, Adamri, Zaramri da Mairamri da Dambiya, Shaan na daya da Shaan na biyu, Makintari, Bulbulin Ngaura da Diwa Jodri.
Wasu Da SUka Samu Tallafin Sabbin Gidaje 500 A Garin Nguro-Soye Wadanda Gwamna Zulum Ya Bayar
Zulum ya ce baya ga gidajen, an bai wa kowanne daga cikin al'ummomin kudi Naira 50,000 da muhimman kayayyaki kamar su tabarmai, katifu, gidan sauro, kayan abinci da kuma kayan amfanin gona, yayin da mata aka basu Naira 25,000 kowacce.
Sabbin Gidajen 500 A Garin Nguro-Soye Wadanda Gwamna Zulum Ya Baiwa Mutanen Da Kungiyar Boko-Haram Ta Koro Yankin
Sauran garuruwan da za a yi gini a nan da watanni biyu zuwa uku inji gwamna Zulum sune, Kumshe, Mayanti da Bula Yobe duk a garin Bama.
Saurari cikakken rahoto daga Ibrahim Ibrahim:
Your browser doesn’t support HTML5
Boko Haram: Zulum Ya Kaddamar Da Sabbin Gidaje 500 Na 'Yan gudun Hijira