GRACE ALHERI ABDU: Me Ya Kai Sanata Da Marin Mata? Kashi Na Daya-Yuli,11, 2019

Grace Alheri Abdu

A karshen makon da ya gabata aka yi ta yayata faifan bidiyon da aka nada inda aka ga dan majalisar dattijai mai wakiltar Adamawa ta arewa a majalisar dattijan Najeriya Elisha Abbo ya rika kakkale wata mace da ke aiki a shagon da mari ya kuma umarci dogarinsa dan sanda ya kama ta. Sai dai ganin yadda aka yi ta zanga zanga da tofin Allah tsine kan batun, dan majalisan ya fito ya bada hakuri yana kuka yana neman gafara.

Shirin Domin Iyali ya tattauna da wadansu mata 'yan gwaggwarmaya dake zaune a nan Amurka Helen Bako dake jihar California da kuma Khuraira Musa wadda ke zaune a birnin NY domin jin matakan da za a iya dauka na ganin haka bata sake faruwa ba.

Saurari bayanan nasu

Your browser doesn’t support HTML5

Sanata da cin zarafin mata-10:00" Pt1

.