Hukumar dake kula da kasuwancin kasa da kasa ta kungiyar tarayyar turai, ta haramatawa Ghana shigar da wasu amfanin gonakinta zuwa kasashen Turai a shekarar 2015. Haramcin ya shafi diyan itace da kayan lambu saboda samun wasu gurbatattun abinci da aka aike dasu Turai.
WASHINGTON DC —
Wannan al’amari ya tada hankalin hukumomin Ghana, ganin yadda sashen noma ke taimakawa tattalin arzikin kasar. Hakan ya kai ga daukar muhimman matakai na neman dalilin da ya haddasa rubewar abincin.
A dalilin haka hukumar kula da ingancin kaya ta Ghana tare da taimakon gwamnati Jamus, suka kirkiro cibiyar inganta diyan itace da sauran kayan lambu da za a rika aikewa dasu kasashen waje.
Wasu manoma sun ce gurbacewar kayan gonar ba daga wurinsu bane. Sun gayawa wakilin Sashen Hausa a Ghana cewa masu sarin kayan daga hannunsu ne suka gurbace domin suna amfani da wasu sanadarai dake gurbata abincin.