Fadar Gwamnatin Taraiyan Najeriya Ta Nuna Damuwarta Matuka Dangane da Sabobin Bayane Dake Fitowa
WASHINGTON DC —
Fadar gwamnatin taraiyan Najeriya, ta nuna damuwata matuka dangane da sabobin bayane dake fitowa akan kudaden da suka bace a asusun ma'aikatan mai na NNPC.
Shugaban kasa Good luck Jonathan, yace ya amince cewa lallai dalar Amurka miliyan dubu goma sun salwanta daga asusun ma'aikatan NNPC.