A daren jiya Litinin ne ‘yan bindiga dauke da muggan makamai suka abka wa garin na Nyalum suka hallaka mutane uku suka yi garkuwa da wasu mata suka kuma jikkata wasu mutanen.
Garin Nyalum dake karamar hukumar Wase a Jahar Filato
Wani mazaunin kauyen da ya bukaci in sakaya sunansa, saboda tsaro yace ‘yan bindiga sun mai da kauyukan nasu fagen dagar yaki.
Yan bindiga
A hirar shi da Muryar Amurka, kakakin rundunar ‘yan sandan Jahar Filato, DSP Alfred Alabo ya tabbatar da aukuwar harin, sai dai yace har lokacin da Muryar Amurka ke magana da shi bai sami cikakken bayani daga DPO'n yankin ba.
Dazukan dake kananan hukumomin Wase da Kanam dake makwabtaka da juna, sun kasance tamkar mafakan ‘yan ta’adda, don haka al’ummar kauyukan ke neman dauki.
Saurare rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5
FILATO: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 3 A Garin Nyalum Ciki Har Da Basaraken Gargajiyan Yankin