A ci gaba da bibiya kan yadda cutar coronavirus ta shafi rayuwar iyali, yau, bakuwar da muka gayyata a shirin Dr Mairo Mandara kwararrar likitan mata, ta yi bayani kan yadda wannan anobar ta sauya yadda aka saba ziyara da kuma zumunci tsakanin iyali da kuma dangi.