DOMIN IYALI: Yadda Annobar Coronavirus Ta Shafi Iyali- Kashi Na Daya, Mayu, 14, 2020

Grace Alheri Abdu

Abinda ya dauke hankalin al’umma a duk fadin duniya shine annobar Coronavirus da ta kama miliyoyin mutane, ta kuma tauye rayuwar kowanne bil’adama ta yau da kullum, a duk inda yake a duniya.

Sai dai duk da irin fadakarwa da ake yi kan wannan cuta, har yanzu mutane da dama suna tababa a kan batun, abinda ya zama da hatsarin gaske da kuma barazana ga ci gaban iyali.

Ta haka shirin Domin Iyali ya gayyaci kwararariyar likitar Mata, Dr. Mairo Mandara kwararrar likitan mata, domin yin Karin haske da kuma fadakar da al’umma kan wannan annoba.

Saurari cikakken shirin

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda cutar Coronavirus ta shafi Iyali:Pt1