Shirin Domin Iyali na wannna makon ya yi nazari ne kan kalubalen da ake fuskanta kan harkokin tsaro a Najeriya bayan sace dalibai da wadansu jami’ai kusan dari uku a makarantar LEA ta Kuriga dake jihar Kaduna, shekaru goma bayan garkuwa da ‘yammata sakandaren Chibok dari biyu da saba’in da hudu.