DOMIN IYALI: Ana Zargin Magidanci Da Bata 'Ya'yansa Kanana-Kashi Na Daya.

Grace Alheri Abdu

A shirin Domin Iyali na yau mun yi hira a wata mata a unguwar Rigassa cikin garin Kaduna wadda ta yi zargin mijinta yin lalata da 'ya'yansu mata kanana biyu 'yan shekara shida da kuma uku, batun da kananan yaran suka nanata a hirarraki da aka yi da su, binciken likitoci kuma ya tabbatar.

Sai dai magidancin ya musanta zargin, ya kuma saki matar da yace tana bata mashi suna. Baya ga haka, ya kai kara kotu da nufin neman a kwatar mashi 'ya'yan daga hannun mahaifiyarsu.

Saurari kashin farko na hirar shirin da mahaifiyar yaran.

Your browser doesn’t support HTML5

An Zarfi mahaifi da lalata 'ya'yansa mata PT1-10:00"