Daga Libiya An Tasa Keyar Wasu 'Yan Najeriya 'yan Masu Zuwa Cirani Gida

Rahotanni da dumi dumin su sun bayyana cewar hukumar kula da harkokin tafiye tafiye ta kasa da kasa ta tasa keyar wasu 'yan Najeriya guda 172 wadanda suka hada mata 6 daga kasar Libiya zuwa gida Najeriya.

An bayyana cewa a cikin tawagar 'yan ci ranin ta hada da wani dan karamin yaro a cikin wadanda aka tasa keyar su zuwa filin jirgin Mitiga dake birnin Tripoli a babban birnin kasar da misalin karfe 4:30 na safe.

Rahotannin sun bayyana cewa kusan dukkan 'yan ci ranin da aka taso keyar su zuwa Najeriya an kama su ne akan hanyar su ta kokarin ketarawa zuwa Turai kamar yadda wasu suka bayyana cewa zasu ne domin neman rayuwa mai kyau.

Ofishin jakadancin Najeriya da hukumomin kasar Libiya ne suka shirya mayar da mutanen gida bayan sun kwashe wasu watan da wasu daga cikin su suka yi a tsare, kuma an mayar masu da kayayyakin su wadanda suka hada da wayar hannu da sauran su a daidai lokacin da suke hanyar komawa kasar da suka fito.