Daga Dan Yaro Ya Hana Ta Barci Kawai Sai Ta Yanke Mai Al'aura

An zargi wata mata mai sun a Liu Tao, da ke zama a unguwar Shaodong dake kasar China da laifin yanke ma wani yaro mai shekaru shidda yatsu da al'aurar sa a sakamakon hana barcin da yayi.

Rahotanni sun bayyana cewar matar tana barci ne a dakin wata 'yar uwarta dake zama a wani gidan haya yayin da yaron ya shiga dakin da take barcin har ya kaiga tashin ta daga barcin.

A cewar rahoton, matar ta tashi ta fitar da yaron waje sa'an nan ta koma ta kwanta ta ci gaba da barci amma sai yaron ya sake komawa ya cigaba da wasa a cikin dakin.

Kamar yadda mujallar Xiaoming ta wallafa, mai makon ta fitar da shi waje kamar yadda ta yi da farko, sai kawai ta lauki wuka da almakashi mai kaifin gaske ta tafka masa yanka a yatsun sa, da fuskar sa da kuma al'aurar sa. Bayanan sun bayyana cewar matar ta arce zuwa unguwar da ta fito bayan aikata wannan danyen aiki.

'yan sanda sun bita har unguwar da take kuma sun kama ta, sai dai a lokacin da aka cafke ta ba'a ga inda ta jefa tsinkin al'aurar ba har sai da aka koma gidan da abin ya afku kafin aka gano guntulen sannan aka garzaya aka kai asoibiti inda ake kokarin janawa.