DA DANGARI: Tarihin Garin Tsagem, Jihar Katsina, Oktoba 29, 2022
Shirin Da Dangari na wannan makon ya kai ziyara garin Tsagem da ke karamar hukumar Mani a jihar Katsina don jin tarihin garin.
WASHINGTON, D.C —
Garin Tsagem ya shahara sosai kuma gari ne na Fulani da Malamai. Basaraken garin Buhari Usman, ya ce garin ya shahara a fannin kiwo da noma kuma har yanzu kaburburan sarakunan garin na baya na nan a wurin Dutsen Gandu.
Duk da shahararsa, garin na fuskantar kalubalen karancin samun ci gaba, musamman ta bangaren hanyoyi da kuma karancin ruwa.
Saurari cikakken shirin wanda Abdul Jani ya gabatar.