DA DANGARI: Tarihin Garin Rigachikun, Kaduna, Afrilu 8, 2023
Bandiagara, Mali
Washington, DC. —
Shirin Da Dangari na wannan makon ya kai ziyara garin Rigachikun da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
Nasiru Yakubu Birnin Yero na gidan rediyon Nagarta a jihar Kaduna ya yi hira da basaraken garin Malam Ishad Ibrahim wanda ya ba da dan takaitaccen tarihin garin, inda ya ce Fulani daga garin Ruma a jihar Katsina ne suka kafa garin.
Galadima Ishad ya kuma ce noma da kiwo su aka san ‘yan garin da su.