Chile Ta Yi ma Mexico Dukar Da Ba A Taba Yi Mata Ba: Ci 7 Da 0 A Gasar Copa America
'Yan wasan Chile sun hadu su na murna a bayan da Edson Puch ya jefa kwallo a ragar 'yan Mexico a wasan kwata fainal da suka buga na gasar Copa America a filin wasa na Levi's Stadium dake Santa Clara, a Jihar California
Dan wasan Chile, Edson Puch (hagu) da dan wasan Mexico Andres Guardado su na neman kwallo a karawar ta su.
Dan wasan Mexico, Javier Hernandez, na biyu daga hagu da Arturo Vidal na kasar Chile (mai sanye da riga mai lamba 8) su na kokawar neman kwallo a lokacin karawar tasu.
Edson Puch na Chile da sauran 'yan wasan kasarsa su na murnar jefa kwallo a raga.
Arturo Vidal na Chile da Hector Herrera na Mexico su na neman kwallo a karawarsu ta kwata fainal a gasar Copa America.
Magoya bayan Mexico, wata cikinsu tana kuka, a bayan da kasarsu ta sha kashi da ci 7 da 0 a hannun 'yan wasan Chile.