Boko Haram Ta Halaka Dakarun Najeriya 13

Wasu dakarun Najeriya a lokacin da suke sintiri a yankin arewa maso gabashin Najeriya

“Sai dai abin bakin cikin shi ne, dakarun Najeriya 13 da wani dan sanda daya” sun rasa rayukansu a lokacin da suke kokarin kaucewa harin.

Mayakan Boko Haram sun halaka wasu sojojin Najeriya 13 da wani dan sanda daya a yankin arewa maso gabashin kasar.

Wata sanarwa dauke da sa hannun mataimakin Darektan yada labarai na rundunar sojin Najeriya, Col. Onyema Nwachukwu, ta ce mayakan na Boko Haram sun kai wa dakarun runduna ta daya harin kwantan-baunar ne a lokacin suke tafiya akan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a jiya Litinin.

A cewar sanarwar, wacce rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter, “zaratan dakarun kasar sun yi arangama da maharan, inda har suka samu kutsa kai ta hanyar da suke tafiya.

“Sai dai abin bakin cikin shi ne, dakarun Najeriya 13 da wani dan sanda daya” sun rasa rayukansu a lokacin da suke kokarin kaucewa harin.

Sanarwar ta kara da cewa, wasu dakarun kasar na can suna ci gaba da bin diddigin maharan domin a kakkabe su.

A wani hari na daban kuma, rundunar soji ta musamman ta “Operation Lafiya Dole” ta ce ta kashe mayakan kungiyar ta Boko Haram da dama, a lokacin da mayakan kungiyar suka kai wani hari a sansanin sojin kasar da ke Kukareta a karamar hukumar Damaturu a jihar Yobe.

“A lokacin da mayakan suka kai hari a sansanin da misalin karfe 6:30 na yamma, sun tarar da fushin dakarunmu wadanda suka far musu suka karkashe su.”

A wannan hari na daban, sojan Najeriya daya ne ya ji rauni a cewar sanarwar.