Bakin Hauren Afirka Sun Isa Gabar Spain Bayan Ceto Su

  • Ibrahim Garba

Wani dan yaro daga cikin bakin hauren da aka ceto

Duk da yawan mutuwa a kogin Bahar Rum da bakin hauren Afirka masu aniyar zuwa Turai ke yi wannan bai hana wasu 'yan Afirka cigaba da daukar kasadar ratsa kogin Bahar Rum don isa kasashen jar fata ba. Na baya-bayan nan su ne wasu kimanin 310 da aka ceto a Bahar Rum.

Wani jirgin ruwa dauke da bakin haure, wadanda akasari 'yan Afirka ne, ya samu isa bakin gabar Spain a yau dinnan Jumma'a, bayan da kasashen Turai da dama su ka hana shi shiga yankin gabarsu, ciki har da Malta da Italiya.

Jirgin ruwan mai suna Open Arm ya ceto bakin hauren ne daura da gabar Libiya a ranar 21 ga watan nan na Disamba.

Jirgin na wata kungiyar agaji ne ta kasar Spain mai suna Proactive Open Arms.

Bakin hauren, wadanda yawansu ya kai 310, sun fice daga cikin jirgin a yau dinnan Jumma'a lullube da jajayen barguna zuwa inda kungiyar Red Cross za ta gwada lafiyarsu.

A baya ma, yayin da jirgin ke tafe da bakin hauren, an amince a kai wani karamin yaro wurin jinya a tsibirin Lampedusa na kasar Italiya.

Haka zalika, ranar Asabar wani jirgi mai saukar ungulu ya dau wata mace da jinjirinta zuwa Malta don a yi jinyarsu