Baiwa Matasa da Mata Matsayin Ministoci

A jahar Neja, ra’ayin ‘yan siyasa ya sha banban akan bayana sunan tsohon mataimakin Gwamnan jahar Ahmed Musa Ibeto, a cikin jerin sunayen da shugaba Buhari ya turawa majalisar.

A yanzu haka ‘yan Najeriya, na ci gaba da yin tsokaci akan sunayen mutanen da shugaba Buhari, ya turawa majalisa domin basu matsayin minista.

A halin yanzu dai yayin da ake jiran kashi na biyu na sunayen sabbin ministocin da shugaba Buhari, ya ce zai turawa majalisar nan gaba masu nazari akan harkokin siyasa na ganin akwai bukatar Karin akalla mata guda uku da kuma matasa ‘yan kasa da shekaru 40, akalla suma guda uku bisa la’akari bisa gaggarumi gudumawar da suka barai wajen kafa sabuwar Gwamnatin Muhammadu Buharin.